Najeriya: An sace ma'aikatan hakar mai
January 19, 2018Lamarin dai ya faru ne tun a yammacin ranar Laraba a cewar Andrew Aniamaka mai magana da yawun 'yan sandan jihar Delta a Tarayyar ta Najeriya, wanda ya ce a halin yanzu ba su da wani cikakken labari kan yadda aka sace wadannan ma'aikata guda biyar, amma kuma tuni sojoji suka baza komarsu domin gano inda aka kai wadannan ma'aikata.
Sai dai wani mazaunin yankin da ya ganewa idanunsa lamarin, ya ce mutanen da aka sace 'yan Najeriya ne kuma suna cikin jirgin ruwa ne bisa hanyarsu ta zuwa wurin aiki lokacin da wasu mutane guda biyar dauke da makamai fuskokinsu a rufe suka kai musu harin.
'Yan awowoyi kadan dai kafin afkuwar lamarin, sai da 'yan kungiyar NDA ta Niger Delta Avengers ta ja hankalin gwamnatin ta Najeriya cikin wata sanarwa, inda ta ce za ta sake komawa ga hare-haren da ta saba.