1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An karfafa matakan yakar annobar Lassa

Uwais Abubakar Idris RGB
January 28, 2020

Masana muhalli sun shiga fafutukar ganin an dakile annobar Lassa da ke yaduwa a Najeriya a daidai lokacin da aka sami bullar cutar a wasu jihohin kasar.

https://p.dw.com/p/3WvFy
Deutschland Robert Koch-Institut S4-Labor in Berlin
Hoto: picture-alliance/dpa/S. Stache

A Najeriya dai dai lokacin da ake ci gaba da daukan matakan kariya ga cutar zazzabin bera ta Lassa wacce ya zuwa yanzu ta bulla a jihohi goma sha daya na kasar, ma’aikatar kula da muhallin kasar ta shigo cikin lamarin inda ta zayyana matakan da yak am ata alumma su dauka domin samun kariya.


Zazzabin bera na Lassa da ke ci gaba da yaduwa a tarayyar Najeriya na zama daya daga cikin manyan kalubale na kula da lafiyar al'umma da ake fama da shi a kasar, domin zazzabin da ke kai ga kisan dan adam, babban al’amari ne ga al’ummar kasar. Danganta ciwon da batun tsafta da karancinta ke sanya berayen da ke yada cutar kara shiga cikin al'umma, lamarin da ya sanya ministan kula da muhalli na Najeriyar Dr Mohammad Mahmoud bayyana matakan da suke fadakar da jama’a a kai.

Symbolbild Ratten
Bincike ya gano cin naman bera ka iya haifar da cutar LassaHoto: Colourbox/G. Dolgikh


Duk da bayanan da aka dade ana yi a kan zazzabin Lassa har yanzu akwai ‘yan Najeriya da dama da ke neman bayani a game da hanyoyi da ake kamuwa da zazzabin. Shekaru fiye da hamsin kenan ana fama da zazzabin Lassa a kasar wanda sai ya yi kamar ya tafi ya sake dawowa, abinda ya sanya kungiyar likitocin kasar bayyana cewa akwai gyara.


Ma'ikatar kula da muhalli ta ja kunnen ‘yan kasar da su guji cin bera musamman a wannan yanayi na kaka da ake kona daji. A yayin da ake ci gaba da gangami na tarba-tarba ga wannan cuta ya zuwa yanzu dai zazzabin na Lassa ya yi dalilin mutuwar mutane 29 yayin da ake ci gaba da yi wa wasu akalla dari da casa'in da tara da suka kamu da cutar magani.