Najeriya: An halaka manoma 8 a jihar Benue | Labarai | DW | 09.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: An halaka manoma 8 a jihar Benue

A Najeriya hukumar 'yan sanda ta jihar Benue ta ce Fulani makiyaya sun kashe wasu mutane takwas a jihar wacce ke a tsakiyar kasar da kuma ke fama da fadace-fadace na tsakanin makiyaya da manoma. 

Kwamishinan 'yan sandar jihar ta Benue Bashir Makama ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa fulanin makiyaya sun kashe mutanen ne a lokacin wani hari da suka kai a daren Litinin washe garin Talatar nan a wasu kauyuka biyu na manoma a yankin Logo na Gabashin jihar ta Benue. Kuma ya ce rikicin ya samu asali ne lokacin da mutanen kauyukan na manoma suka yi yinkurin hana wa makiyayen yin kiwon dabbobinsu a cikin gonakkinsu. 

Jihar Benue dai ta yi kaurin suna wajen fadace-fadacen manoma da makiyaya inda ko a shekarar da ta gabata, an halaka daruruwan mutane tare da kone gidaje kimanin dubu a wani kazamin fadan da ya barke tskanin manoman da makiya ya a garin Agatu na cikin jihar.