Najeriya: An gudanar da bikin sallar layya lafiya | Zamantakewa | DW | 15.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Najeriya: An gudanar da bikin sallar layya lafiya

A Najeriya sabanin yadda ta kasance a shekarun baya inda aka fuskanci hare-haren Kungiyar Boko Haram a wasu yankuna a ranar salla, a shekara bana sallar layya ta wakana lami lafiya.

Al'ummar Musulmin Najeriya ta gudanar da bukukuwan sallar layya na shekarar bana cikin konciyar hankali da lumana, sabanin yadda a shekarun baya hare-haren Kungiyar Boko Haram suka lalata armashin bukukuwan. Kuma wani abin sha'awa shi ne irin yadda bikin sallar ya kasance wata dama ta kara karfafa dankwan zumunci tsakanin mabiya addinin Krista da Musulmi a Najeriyar.

Sauti da bidiyo akan labarin