1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amnesty ta koka da hukumomin tsaron Najeriya

Uwaisu Abubakar/GATFebruary 1, 2016

Kungiyar Amnesty International ta nuna damuwa kan mayar da daya daga cikin manyan hafsoshin sojan da ta zarga da aikata manyan laifuka, a yakin da ake da Boko Haram bakin aikinsa

https://p.dw.com/p/1Hn3X
Nigeria Symbolbild Armee Soldaten Offiziere
Hoto: picture-alliance/AP Photo/O. Gbemiga

Kungiyar kare hakin dan Adam din ta Amnesty International ta ce duk da alkawarin da mahukuntan Najeriyar suka yi na dakile sake afkuwar irin wannanmtsala a harkar tsaron, sai gashi an mayar da Major Janar Ahmadu Muhammad bakin aikinsa. A watan Yunin shekarar da ta gabata ta 2015 dai, kungiyar ta ambato sunansa da wasu manyan hafasoshin guda takwas da ta bukaci a gudanar da bincike a kansu bisa zargin hannunsu a kisan fiye da firsinonin 8000 a Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno da ke Najeriyar.

Abin da aka tsammata daga gwamnati

Nigeria Soldaten
Hoto: I. Sanogo/AFP/Getty Images

Abin da ya fi daga hankalin kungiyar dai shi ne yadda bayan alkawarin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi na cewa lallai zai gudanar da bincike, a kan zarge-zargen da aka yi bayan wallafa wancan rahoton domin kawo karshen kawar da kai da ake yi a kan wadanda ake zargi da aikata laifuffuka irin wadannan. Mr Daniel Eyre shi ne jami’in kungiyar ta Amnesty International ya bayyana yadda suke kallon lamarin da abin da suke son ganin gwamnatin ta yi.

Ya ce "Abin da muke cewa shi ne kada a mayar da Major Janar Ahmadu Muhammad a bakin aikinsa domin ya na fuskantar zargin aikata laifuffukan yaki, ba shi kadai ba ma muna cewa dukkanin sauran mutanen da muka ambata su ma a dakatar da su, muna sane cewa a cikinsu akwai wadanda ba a san inda suke ba wasu sun yi ritaya. Muna son ganin gwamnatin Shugaba Buhari ta cika alkawari na hukunta su kamar yadda ta yi a baya, ba wai mu ji an mayar da shi bakin aiki ba ya na ma jira ne kawai a tura shi wajen aiki."

Matakin da ya kamata a dauka

Zargin kawar da kai na kin daukar mataki a kan masu aikata laifuffuka musamman manyan jami’an soja ya kasance lamarin da kwararru a harkar shari’a ke kashedi da ci gaba da faruwarsa a yanayin da Najeriyar ke ciki. Ko wacce illa wannan ke da shi ga yadda ake kallon Najeriyar a yanzu? Barrister Mainasara Umar masani ne a kan dokoki a Najeriyar.

Nigeria Armee Task Force gegen Islamisten Boko Haram
Hoto: Getty Images/AFP

Ya ce "Duk wani wanda yake da hannu ba ma kotun Najeriya ba, kotun ICC ya kamata a kai shi. Domin idan mutum na da hannu aka mai da shi kan kujera zai iya kawo nakasu ga wasu bayanai da takardun bayanai wadanda ke karkakashin wannan hukuma ta soja. Dan haka hukumar soja ta yi hattara ta san irin abin da ta ke yi da kuma hadarin da ke tattare da wani wanda ake zargi a ce an barshi ya na zaune a kan kujerarsa"

To sai dai al'ummar kasar na cike da kyakyawan fata na shiga yanayin kowa ya yi za’a yi mashi abin da ke samar da sabon babi a harkar hukunta masu laifuffuka a Najeriyar da ake wa kallon na iya maido da kamanta adalci. A yayin da kotun kasa da kasa da ke hukunta wadanda suka aikata laifuffukan yaki ke nazarin hallacin fara bincike a kan wadanan zarge-zarge da kungiyar Amnesty ta yi, za’a sa ido a ga matakin da gwamnatin Najeriyar za ta dauka musamman alkawarin da Shugaba Muhammadu Buhariu ya yi cewa lallai za’a gudanar da bincike a kan lamarin.