Najeriya: Alkalin Alkalai ya yi murabus | Labarai | DW | 05.04.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: Alkalin Alkalai ya yi murabus

Rahotanni daga Najeriya na cewar Alkalin Alkalan kasar wanda aka dakatar daga bakin aiki bisa zargin kin bayyana kadarorinsa wato Walter Onnoghen ya mika takardarsa ta yin murabus.

Lauyan Mr. Onnoghen, Adegboyega Awomolo ne ya tabbatar da wannan labarin a hirarsa da kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP, inda ya ce tun a jiya ne Alkalin Alkalan ya ajiye aiki.

A kwanakin da suka gabata ne dai hukumar kula da harkokin shari'a ta kasar NJC ta bai wa Shugaba Muhammadu Buhari shawarar sauke Onnoghen din daga bakin aiki, wanda a halin yanzu ya ke fuskantar shari'a a gaban kotun da'ar ma'aikata kan batun bayyana kadarorinsa.