Najeriya za ta daina ba da tallafi a kan mai
November 25, 2021Talla
Wannan al'amari dai na janye tallafin da zai fara aiki a cikin sabuwar shekara 2022 ya janyo martanin al'ummar kasar cikin bacin rai wadanda ke korafin cewar kasar za ta kara shiga wani mawuyacin hali. A bayyane take a fili janye tallafin zai sanya man fetir yin tsada a Najeriyar, inda kamfanin albarkatun main a kasar ya dade da hasashen zai iya kai Naira 400 kowace lita guda, wannan ya sanya gwamnatin tsara bai wa marasa galihu milyan 30 zuwa 40 talafin kudin shiga mota na Naira dubu biyar. Bankin duniya ya dade da nuna cewa tallafin mai ne ke yi wa Najeriya dabaibay, abin da za’a sa a ga jnaye tallafin zai zaburara da tattalin arzikin Najeriya. Daga kasa mun tanadar muku a rahotanni.