Nairobi na karbar bakuncin taron lafiyar iyali | Labarai | DW | 11.11.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nairobi na karbar bakuncin taron lafiyar iyali

Matan Afrika sun fi na kowanne nahiya amfani da tsarin iyali na zamani don rage haihuwa kamar yadda wani rahoto na Kungiyar da ke kula da shirin tsarin iyali a duniya ya nunar.

A wani sabon rahoto na wannan Litinin, an gano yadda matan Afrika suka fi na kowanne nahiya amfani da tsarin iyali na zamani don rage haihuwa. Rahoton na Kungiyar da ke kula da shirin tsarin iyali ta duniya, ya nunar cewa, mata a sassan nahiyar Afirka kimanin miliyan dari uku da goma sha hudu ne suka rungumi tsarin iyali daga cikin miliyan dari tara da ashirin da shida da ke amfani da tsarin a sassan duniya.

An tattara bayanan ne na kasashen duniya akalla sittin da tara, inda kasashen Afrika 41 ke gaba, 21 na nahiyar Asiya ke biye sai nahiyar Latin Amirka yayin da Gabas ta Tsakiya ke can kasa. An baiyana sakamakon rahoton ne a wani taro kan lafiyar iyali da ke gudana a birnin Nairobin Kenya. Taron ya fuskanci kalubale daga masu zanga-zanga na cocin Katolika da ke adawa da tsarin iyalin.