Nadin Shaikha Haya shugabar taron MDD | Siyasa | DW | 19.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Nadin Shaikha Haya shugabar taron MDD

An nada Shaikha Haya 'yar kasar Bahrain domin shugabancin Babbar Mashawartar MDD

Tun dai a cikin karnin da ya wuce ne aka fara samun kungiyoyin fafutukar tabbatar da hakkin mata a kasar Bahrain, ita kuma Shaikha Haya ta taka muhimmiyar rawa wajen karfafa ilimin mata da ba su kafar shiga zaben majalisun kananan hukumomi. Kuma mata a kasar Bahrain sun samu ci gaba matuka ainun fiye da takwarorinsu a sauran kasashen Larabawa na yankin Gulf. To sai dai kuma nadin Shaikha Haya da aka yi domin shugabancin babbar mashawartar MDD ya haifar da zazzafar mahawara tsakanin ‘yan siyasar kasar a game da wuce gona da iri dangane da manufofin canje-canje na siyasa da tsarin zamantakewa a kasar. A lokacin da take bayani Ghada Jamshir daya daga cikin masu fafutukar kare hakkin mata a kasar Bahrain ta ce nadin da aka yi wa Shaikha Haya ba zai sanya a yi watsi da zazzafar akidar addini dake ci gaba da yaduwa a kasar, sai ta kara da cewar:

“’Yan salafiya dake da zazzafan ra’ayin rikau a Bahrain na taka muhimmiyar rawa wajen neman dakatar da ci gaban da mata ke samu a wannan kasa. Babban misali game da haka shi ne gazawar da gwamnati tayi na bayyana matsayin mata a kasr duk da cewar tana da ikon yin haka ta kan majalisar dokoki. ‘Yan gata, wadanda ke da alaka ta kut-da-kut da gwamnati da dangin gidan sarauta ne kawai ke da kyakkyawan matsayi.”

Wannan bayanin nata yayi daura da ikirarin da ake yi na cewar tun abin da ya kama daga shekarar 1999, wato tun lokacin da sarki Hamad Ben Issa Aal Khalifat ya karbi ragamar mulki kasar Baharain ke samun canjin manufofinta daga tushensu. Amma duk da haka nadin Shaikha Haya da aka yi domin shugabancin babbar mashawartar MDD babban ci gaba ne kuma abin murna da farin ciki ga mata a kasar Bahrain, kamar yadda aka ji daga bakin Nada Al-Hifaz ministar kiwon lafiya ta kasar, wadda ta kara da cewar:

Ina mai murna da farin ciki da kuma alfahari, saboda kasancewar ita ce wata mace balarabiya ta farko da ta karbi wannan muhimmin mukami na siyasa a matsayi na kasa da kasa, kuma a lokaci guda tana wakiltar kasar Bahrain. Bugu da kari na san Shaikha Haya Bint Rashid sosai-da-sosai a matsayin mace da ta san makama.”

A jawabinta na bude taron babbar mashawartar ta MDD Shaikha Haya tayi kira da a kara yin bobbasa a fafutukar yaki da talauci a duk fadin duniya. Kazalika ta ce zata kara karfafa goyan bayanta wajen tabbatar da hakkin mata tare da kawar da wariyar da ake nuna musu a fannoni na ilimi da kiwon lafiya da sauran al’amuran da suka shafi rayuwa ta yau da kullum. Ko shakka babu kuwa nadin da aka yi wa jami’ar a wannan babbar kafa ta MDD zai haifar da gagarumar mahawara a game da matsayin mata a kasashen Larabawa da na Musulmi baki daya.