1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nadin ministoci ya bar baya da kura

Abdullahi Tanko Bala
July 25, 2019

Watanni biyu bayan rantsar da shi a wa'adin mulki karo na biyu shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada ministoci 43 sai dai nadin ministocin ya bar baya da kura saboda karancin mata da matasa a majalisar ministocin.

https://p.dw.com/p/3Mj7L
Nigeria Kabinett Muhammadu Buhari Präsident
Hoto: Reuters/A.Sotunde

Shugaba Buhari dai ya shafe watanni biyu bayan kama aiki a wa'adinsa na biyu ba tare da girka gwamnati ba sai dai daga cikin sunayen mutane 43 da ya mika wa majalisar dokokin domin amincewa bakwai daga cikinsu ne kacal mata sannan kuma babu matasa sosai a cikin ministocin lamarin da ya janyo cece-kuce a tsakanin 'yan kasar.