1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Na hannun daman Merkel ya rasa matsayinsa

Abdullahi Tanko Bala
September 25, 2018

A wani yanayi na ba zato ba tsammani Volker Kauder wani na hannun daman shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ya rasa matsayinsa na jagorancin rukunin 'yan jam'iyyar CDU a majalisar dokoki.

https://p.dw.com/p/35UT4
Koalitionsverhandlungen von Union und SPD
Hoto: picture-alliance/dpa/B. Pedersen

Wani babban na hannun daman shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ya rasa matsayinsa na jagorancin rukunin 'yan majalisar dokoki na jam'iyar CDU a wata kuri'a cikin gida da 'yan majalisar suka kada lamarin da ke nuna kalubale da kuma raunin shugabanci da Merkel ke fuskanta.

Volker Kauder wanda ya dade yana jagorantar rukunin 'yan majalisar dokoki na Jam'iyyar CDU ta Angela Merkel da abokiyar kawancenta ta CSU har tsawon shekaru 13 ya sha kaye a zaben neman tazarce kan shugabancin rukunin inda aka zabi abokin hamaiyarsa Ralph Brinkhaus wanda ba a san shi ba sosai.

Sakamakon wanda ya bada mamaki ya nuna Volker Kauder ya sami kuri'u 112 yayinda abokin hamaiyarsa Ralph Brinkhaus ya sami kuri'u 125.

Wannan sakamako dai da zo da ba zata na zama babban koma baya ga Angela Merkel, kwana guda bayan da aka tilasta mata amincewa da kura kuran da ta tafka kan yadda ta tafiyar da rikicin da ya dabaibaye shugaban hukumar leken asiri mai barin gado.