Myanmar: Za a mayar da ′yan Rohingya gida | Labarai | DW | 23.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Myanmar: Za a mayar da 'yan Rohingya gida

Fiye da 'yan gudun hijirar Rohingya 620,000 ne suka tsallake zuwa Bangaladash bayan da soja suka kaddamar da hare-hare kan masu tada kayar baya a cikinsu.

Kasar Myanmar da Bangaladash sun kulla yarjejeniya a wannan rana ta Alhamis matakin da zai bude kofa a kokari na mayar da 'yan Rohingya Musulmi da suka kauracewa jihar Rakhine gida, kamar yadda jami'ai suka nunar. Wannan dai na zuwa bayan da rikicin 'yan gudun hijira ya yi tsamari a kasar wanda al'ummar duniya suka karkata a kanta.

Fiye da 'yan gudun hijirar Rohingya 620,000 ne suka tsallake zuwa Bangaladash bayan da soja suka kaddamar da hare-hare kan masu tada kayar baya a cikinsu, kana suka dangana da aika-aikar da ko mahukuntan birnin Washington a wannan mako suka ce kokari ne na kawar da wata al'umma a doran kasa.

Bayan makonni ana sa toka sa katsi bangarorin biyu a Myanmar sun cimma matsaya tsakanin jagorar al'umma  Aung San Suu Kyi  da ministan harkokin wajen Bangaladash Mahmood Ali. Babu dai karin bayanai kan abubuwan da yarjejeniyar ta kunsa.