Myanmar: MDD na son a gyara sansanoni | Labarai | DW | 24.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Myanmar: MDD na son a gyara sansanoni

MDD ta bukaci wannan dama ne domin inganta sansanonin da ta gina wa dubban musulman Rohingya da ke gudun hijira a kasashe makobta domin ba su kwarin gwiwar dawowa kasarsu.

Wata tawagar kasa da kasa da ta ziyarci wasu sansanonin da ke kusa da kan iyakar kasara Myanmar da Bangaledesh sun ce gidajen jama'a ba sa kan tsarin da dan adam zai yi rayuwa a ciki.

Gwamnatin Myanmar na ci gaba da jan kafa wajen tantance dubban 'yan kasar da ake shirin maido su gida daga kasashen da suke gudun hijira, amma MDD ta nun shakku kan ingancin tsaro kan rayuwar wadanda za a dawar.

Hukumomin kula da 'yan gudun hijira na MDD sun kiyasta sama da musulman Rohingya dubu 600 rikicin jihar Rakhine ya tilasta musu tserewa zuwa kasar Bangaledesh tun a watan Agustan shekarar 2017.