1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutuwar Winnie Mandela a jaridun Jamus

Lateefa Mustapha Ja'afar | Abdul-raheem Hassan
April 6, 2018

Sauyin shugabanci a Saliyo da kasar Habasha da kuma mutuwar tsohuwar matar Mandela sun dauki hankalin jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/2vceV
Südafrika Winnie Mandela
Hoto: Imago/Gallo Images

Jaridar die Tageszeitung a sharhinta mai taken "Tsohon jagoran juyin mulki Julius Maada Bio ya lashe zaben shugaban kasa a Saliyo." A shekarar 2012 Julius Maada Bio ya fara tsayawa takara a lokacin yana soja mai ritaya yana da shekaru 47. A wancan lokacin ya fadi zabe, sai dai tsawon shekaru biyar bayan faduwa zaben Julius Bio ya cimma burinsa na zama shugaban kasa. A ranar Laraba 04 ga wtaan Afirilun 2018 Hukumar Zaben kasar Saliyo ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa zagaye na biyu da aka gudanar a kasar cikin watan Maris, inda ya kayar da abokin takararsa na jam'iyya mai mulki APC Samura Kamara. Sa'o'i kalilan da bayyana sakamakon zaben, ya yi rantsuwar kama mulki na tsahon shekaru biyar, inda ya gaji Ernest Bai Koroma na jam'iyyar APC da ya kwashe shekaru 10 yana kan karagar mulki. Yana da shekaru 27 ya kasance guda daga cikin sojojin da suka yi juyin mulki a shekara ta 1992, inda suka kifar da gwamnatin farar hula karkashin jagorancin Joseph Saidu Momohs na jam'iyyar APC, da suka zarga da mulkin kama karya. Bayan shekaru hudu a shekara ta 1996 ya jagoranci juyin mulki, inda ya kifar da gwamnatin Captain Valentine Strasser da suka yi juyin mulkin 1992 tare, inda ya yi juyin mulki na takaitaccen lokaci. Al'ummar kasar dai na yi masa lakani da baban Demokaradiyya. 

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung ta rubuta sharhi mai taken "Fatan Sasantawa" inda tace sabon Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya fito da sabon tsari. Sabon Firaminstan Habashan bai iya yin bayani kan dukkan matsalolin kasar ba a jawabinsa na farko bayan da ya yi rantsuwar kama aiki, sai dai ya yi jawabi mai rasta zukata inda ya yi alkawarin samun 'yanci da kuma cikakkiyar demokaradiyya a kasarsa. Abiy na zaman Firaminista na farko daga kabilar Oromo masu rinjaye a Habasha. Tsawon shekaru Uku kenan matasa 'yan kabilar Oromo na yin zanga-zanga sakamakon matsalar tattalin arziki da ake fama da shi a kasar, da kuma adawa da yadda 'yan kabilar Tigray da suka kasance kaso shida kacal na al'ummar kasar suka mamaye bangaren sojojin kasar. An dai samu ci-gaba sosai ta fannin tattalin arziki a kasar cikin 'yan shekarun baya-bayan nan. Sai dai bai wadatar da baki dayan al'ummar kasar da yawansu ya kai miliyan102 ba. Mai shekaru 41 a duniya, Abiy na zaman shugaban da ake fatan zai tabbatar da ganin an samu sulhu a kasar bayan kwashe tsahon shekaru tana fama da rikici. A shekara ta 1991 Abiy ya kasance guda daga cikin wadanda suka kawo karshen mulkin sojojin kasar da ke goyon bayan tsarin kwamunisanci. Jaridar ta ce koda yake ya kasance tsohon soja, amma al'ummar Habasha na da kyakkyawan fata na kawo sauyi a kansa.

A nata sharhin jaridar Berliner Zeitung mai taken "Matar da ake wa kallon uwa ga al'ummar Afirka ta Kudu Winnie Mandela ta mutu" Marigayiya Winnie Mandela na zaman tsohuwar mata ga tsohon shugaban kasar marigayi Nelson Mandela da ya jagoranci gwagwarmayar yaki da wariyar launin fata a Afirka ta Kudu. Winni Fred Madikizela-Mandela ta mutu ne a ranar Litinin 3 ga watan Afirilun shekarar 2018 a birnin Soweto tana da shekaru 81 a duniya, bayan doguwar jinya. Ita dai Winnie Mandela ta sha fadi tashi bayan da aka kama tsohon mijinta Nelson Mandela tare da yi masa daurin rai da rai. A matsayinta na 'yar gwagwarmaya, Winnie Mandela ta ci gaba da fafutuka har tsahon shekaru 27 da mijinta ya kwashe a gidan kaso kafin a sako shi.