Mutuwar tsohon Firaministan Isra′ila | Siyasa | DW | 12.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Mutuwar tsohon Firaministan Isra'ila

Tsohon Firaministan Isra'ila Ariel Sharon ya mutu bayan da ya kwashe shekaru takwas a kan gadon asibiti cikin halin dogon suma.

Ariel Sharon dai ya mutu ne yana da shekaru 85 a duniya a wani asibiti da ke kusa da birnin Tel Aviv, kuma mutane da dama na bayyana shi a matsayin wani mai taurin kai kuma ɗan ra'ayin riƙau, yayin da a kan yi masa laƙabin da gwarzo. Dabi'unsa sun sanya ya tashi daga abin so da girmamawa ya zuwa abin ƙyama da tsana a yankin Gabas ta TSakiya. Ga dukkan 'yan Isra'ila dai suna kallonsa a matsayin gwarzo a yaƙn Yom Kippur da aka fafata a shekara ta 1973 yayin da a hannu guda kuma Palasɗinawa ke kallonsa a matsayin wanda ya aikata kisan kiyashi a sansanonin Sabra da Shatila.

An haifi Ariel Scheinermann Sharon da aka sani da Arik a birnin Tel Aviv a shekara ta 1928. Iyayensa Yahudawa ne 'yan asalin gabashin Turai kuma sun samu sunan Sharon ne daga inda suka yadda zango. A kan dai danganta rayuwar Sharon da tarihin sojojin sabuwar ƙasar Isra'ila. A yayin yaƙin neman 'yancin kai da ake kira da yaƙin farko tsakanin ƙasashen Larabawa da Isra'ila, da aka fafata a shekara ta 1948 ya taka rawa a yaƙin a matsayin kwamandan askarawan soji. A shekara ta 1953 ya kafa wata ƙungiyar haɗaka da ta ƙware kan juyin-juya hali, biyo bayan wani hari da mayaƙan Palasɗinawa suka kai, shekaru biyu bayan nan kuma sun samu nasarar kutsa kai cikin ƙasar Masar ba tare da izini ba wanda hakan ya ba su damar samun nasara a kan Masar ɗin. Yayin da yake cikin kakin soja an bayyana Sharon a matsayin daya daga cikin ƙwararrun kwamandojin sojoji a filin daga.

Daga soja zuwa farar hula

Kamar dai yadda tarihin mafiya yawan 'yan siyasar ƙasar ta Isra'ila ya nunar, shi ma Sharon ƙwarewarsa a fannin soja ta taimaka masa wajen shiga harkokin siyasar Isra'ilan da kafar dama inda aka zaɓe shi a matsayin ɗan majalisar wakilai daga jam'iyyar LIkud ta masu ra'ayin mazan jiya, yayin da kuma ya rike mukaman minstan gona da kuma na tsaro.

A wanna lokacin ne kuma Isra'ila ta fara ƙokarin mamaye ƙasar Lebanon, a wani yunƙuri na fatattakar ƙungiyar Palestinian Liberation Organization wato PLO daga ƙasar Isra'ilan. Sai dai kuma bayan da 'yan ƙungiyar ta PLO suka janye, Kiristoci da ke ɗauke da muggan makamai waɗanda ke goyon bayan Isra'ilan sun kai musu farmaki a sansanoninsu da ke Sabra da Shatila a birnin Beirut na Lebanon tare kuma da yi musu kisan kiyashi. Kisan kiyashin dai ya afku ne a wani yanki da ke ƙarkashin ikon ƙasar ta Isra'ila wanda kuma ya janyo suka daga al'ummomin ƙasa da ƙasa.

Kafa kwamitin bincike.

Wani kwamitin ƙasar Isra'ilan da aka ɗora wa alhakin gudanar da bincike kan kisan kiyashin, ya tabbatar da cewa Sharon shi ke da alhakin kisan, wanda hakan ya sanya ya sauka daga muƙaminsa na minstan tsaro a shekara ta 1983, sai dai kuma ya ci gaba da kasancewa a majalisar zartasawar ƙasar a matsayin wani minsta da ba shi da tasiri. Amma hakan bai dakusar da fitilar da ke haskawa a kan al'amuran siyasar Shron ɗin ba, inda ya sake samun nasarar zamowa ministan harkokin ƙasashen ƙetare da na kasuwanci da kuma na gine-gine kafin daga bisani a zaɓe shi a matsayin Firaminsta a shekara ta 2001.

Sharon dai a tsahon rayuwarsa ya kasance mai zafi a kan Palasɗinawa, yana mai cewa kare ƙasar Isra'ila shi ne a sahun gaba a wajensa. A ko da yaushe ya kasance mai suka da kuma ƙin amincewa da samar da ƙasar Palasɗinu mai cin gashin kanta da kuma kauracewa duk wani yunƙuri na sasantawa dangane bai wa Palasɗinun 'yancin cin gashin kai. Ya kuma kasance a koda yaushe yana kara faɗaɗa ƙasar Isra'ila inda bai ji ƙungiyar kutsa kai tare da mamaye birnin Kudus ba wanda ya janyo yakin Intifada na biyu da Palasɗinawan suka kwashe tsahon shekaru hudu da rabi suna fafatawa da Iara'ilan.

A daf da ƙarshen wa'adin mulkinsa Sharon ya ɗan rage girman kai da kuma wasu daga cikin halayensa. Ya bai wa sojojin ƙasarsa umurnin janyewa daga yankin Zirin Gaza da kuma rushe gidajen Yahudawa 'yan kama wuri zauna da ke wannan yanki. A ranar huɗu ga watan Janairun shekara ta 2006 ne Sharon ya tsinci kansa cikin halin rai kwa-kwai -mutu kwa-kwai wanda hakan ya tilasata wa mataimakinsa Ehud Olmert ɗarewa kan karagar mulki. Ya dai kasance cikin wannan hali na rashin sanin inda kansa ya ke har tsahon shekaru takwas kafin ya mutu a ranar 11 ga wannan wata na Janairu da muke ciki.

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto

Mawallafiya Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Abdourahamane Hassane

Sauti da bidiyo akan labarin