Mutuwar dalibai a wani sabon hari a Yobe | Labarai | DW | 29.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutuwar dalibai a wani sabon hari a Yobe

Wasu da ake zargin masu kaifin kishin addini ne sun hallaka kimanin dalibai 50 a wata makaranta a yankin Arewa maso gabashin Tarayyar Najeriya.

Ya zuwa yanzu kimanin dalibai 50 ne ake fargabar sun rasa rayukansu, sakamakon harin da wasu da ake zargin masu kaifin kishin addini ne, suka kai a wata Kwalejin Nazarin Aikin Gona a garin Gujba dake jihar Yobe, a arewa maso gabashin Tarayyar Najeriya.

Shugaban makarantar Molima Idi Mato ne ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, wasu mutane dauke da makamai cikin motoci da babura, sun kai hari da misalin karfe daya na daren jiya a makarantar, inda suka budewa dakin kwanan dalibai maza wuta tare da hallaka daliban da dama wanda shekarunsu ba su wuce 18 zuwa 22 a duniya ba.

Ya zuwa yanzu dai jami'an tsaro na ci gaba da kokarin gano gawarwaki, tare kuma da kai wadanda suka jikkata zuwa babban asibiti na Damaturu babban birnin jihar ta Yobe.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe