1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Girgizar kasa ta kashe kimanin mutun dubu a Afghanistan

Abdoulaye Mamane Amadou
June 23, 2022

Ana cigaba da aikin ceto a yankin Kudu maso gabashin Afghanistan bayan mummunar girgizar kasa da ta yi sanadiyar mutuwar mutun kimanin dubu da raunata wasu dubu da 500.

https://p.dw.com/p/4D6N7
Afghanistan
Hoto: Bakhtar News Agency/AP/picture alliance

Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da kai kayayakin agaji da suka hada da abinci da maganguna a yankunan da iftila'in ya faru mai iyaka da kasar Pakistan.

Batun sake tsugunar da mutane da suka tsira da samar masu da ruwan sha a cikiin gaggawa na daga cikin muhimman bukatun da ke gaban kungiyoyin agaji a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Kungiyar Tarayyar Turai da Amirka sun bayyana anniyarsu ta kai daukin gaggawa ga al'ummar fghanistan, bayan da suka nuna kaduwa kan mummunan girgizar kasar.

Wani mai suna Ramiz Alakbarov da ke yankin na kudancin Afghanistan, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewar da akwai kimanin gidaje fiye da dubu biyu galibi wadanda aka gina da laka da suka ruguje, sakamakon girgizar kasar mai karfin maki "5,9".