Mutum miliyan uku na bukatar abinci a Afirka ta Yamma | Labarai | DW | 09.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutum miliyan uku na bukatar abinci a Afirka ta Yamma

Ministocin noma na kasashen Kungiyar UEMOA masu amfani da kudin bai daya na Cefa sun yi shelar bukatar tallafin abinci cikin gaggawa a kasashe takwas na Afirka ta Yamma domin kauce wa fadawa matsalar yinwa. 

Ministocin noma na kasashe mambobin Kungiyar UEMOA ta kasashe masu amfanin da kudin bai daya na Cefa sun yi gargadin cewa mutane kimanin miliyan uku ne a yanzu haka ke bukatar taimakon abinci a cikin gaggawa a kasashe takwas na Afirka ta Yamma domin kauce wa fadawa matsalar yinwa. 

Sun bayyana wannan kira nasu ne a sanarwar bayan taron da suka gudanar a wannan Jumma'a a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar inda suka ce mutanen na bukatar abinci ne musamman a watannin Yuni zuwa Agusta. 

Ministocin sun bayyan damuwarsu a game da yanayin da kananan yara suke ciki na barazanar tamowa musamman a Arewacin kasar Mali da kuma a yankin Kudu maso Gabashin kasar Nijar wanda ke fama da matsalar tsaro da ke da nasaba da hare-haren Boko Haram.