1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutum biyu sun mutu a hari da wuka a kasar Finland

Ramatu Garba Baba MNA
August 18, 2017

A kasar Finland mutum biyu sun mutu wasu shida sun sami rauni a wani hari da aka kai da wuka a kan jama'a, lamarin ya sa hukumomi karfafa tsaro a duk sassan kasar.

https://p.dw.com/p/2iUEA
Finnland Polizeisperrung Symbolbild
Hoto: Getty Images/AFP/Lehtikuva/H. Rissanen

A kasar Finland mutum biyu sun mutu wasu shida sun sami rauni a wani hari da aka kai da wuka a kan jama'a, abinda ya sa hukumomi karfafa tsaro a duk sassan kasar, al'amarin ya auku ne a wannan juma'a a birnin Turku da ke yammancin kasar, shugaban kasar Sauli Niinisto ya halaci taron gudanar da addu'oi ga wadanda suka rasa rayukansu. 

A sanarwar da ma'aikatar tsaron kasar ta fitar ta ce 'yan sanda sun yi nasarar harbe daya daga cikin maharan a yayin da ake ci gaba da farautar sauran da suka tsere wa jami'an tsaro. Kawo yanzu dai wadanda suka jikkata na samun sauki a asibiti, ba a kuma kai ga  tantance ainihin dalilin kai harin ba, ko kuma ya na da nasaba da harin ta'addanci.