Mutum 33 sun halaka a hadarin jirgin ruwa a Najeriya | Labarai | DW | 15.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutum 33 sun halaka a hadarin jirgin ruwa a Najeriya

Rahotani daga Najeriya na cewa wasu mutane akalla 33 ne suka halaka a wani hadarin jirgin ruwa da ya auku a jahar Kebbi da ke Arewa maso Gabashin kasar.

A wata sanarwar da hukumar agaji ta NEMA shiyar Arewa maso Gabashin Najeriyan ta fitar, ta ce jirgin ruwan ya na dauke da mutane fiye da kima a yayin da hadarin ya auku, kuma baya ga mutane talatin da uku da aka yi nasarar zakulo gawarwakinsu daga cikin ruwa akwai wasu mutane ashirin da uku da suka bata, hadarin ya auku ne a safiyar wannan Laraba inji wani jami'in hukumar ta NEMA.