1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutanen da suka mutu a Chemnitz sun karu

Mouhamadou Awal Balarabe
August 28, 2018

Yayin da 'yan sanda suka ce wadanda suka mutu a zanga-zangar sun kai 20, ministar shari'a ta Jamus ta yi gargadi game da daukar doka a hannu a rikicin da ke gudana a Chemnitz da ke gabashi,

https://p.dw.com/p/33tfG
Deutschland Demonstration der rechten Szene in Chemnitz
Hoto: picture-alliance/dpa/S. Willnow

Rundunar 'yan sandan Jamus ta bayyana yawan mutanen da suka jikkata a zanga-zangar kin jinin baki a garin Chemnitz na gabashin kasar daga mutane shida zuwa 20. Cikin wata sanarwa da ta fitar a wannan Talatar, rundunar ta ce 'yan sanda biyu, da masu akidar kyamar baki da masu zanga-zanga tara sun ji rauni a cikin rikicin.

Ministar shari'a ta Jamus Katharina Barley ta yi kira ga hukumomin Jihar Saxon da ke gabashin kasar da su c gaba da gurfanar da masu akidar kyamar baki da suka aikata laifukan a tashin hankalin da ya barke a garin Chemnitz. Tuni dai Jamusawa suka fara nuna fargaba dangane salon da zanga-zangar ke dauka.

 Mutuwar wani dan shekaru 35, wanda ake zargi wani da ke da tushe da Siriya da Iraki ne ta haddasa wannan tashin hankalin.