Mutane uku sun hallaka a Sokoto | Labarai | DW | 13.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane uku sun hallaka a Sokoto

Musayar wuta tsakanin sojoji da 'yan bindiga ya hallaka mutane uku a jihar Sokoton Najeriya, waɗanda ake zargi 'ya'yan ƙungiyar Boko Haram ne

Rundunar sojin Najeriya dake sokoto a safiyar yau ta share sao'i bakwai tana musayar wuta, bayan da ta kai wani samame sabbin gidajen gwamnati da ta baiwa ma'aikata na Bado Quaters, inda wasu suke kyautata zaton cewa yan kungiyar Boko Haram ne da suka fito daga Jihar Bauchi.

Rahotanni sun ce an kashe uku daga cikin su an kuma kama wata mata guda da yaran su shidda a lokacin samamen.


Hukumomin sojin sun yi amfani da wani rahoton sirri da suka samu ne suka kai samame tun karfe 4 na safiyar yau Labara. A lokacin samamen an tarar da makamai ƙirar zamani da mutanen ke amfani da su.


Yanzu haka rundunar hadin gwiwa na soji da yan sanda a Sokoto sun samu tarwatsa mutanen sun kuma rusa gidan nasu. Babban comandar sojin Najeriya a Sokoto Muhd Tasiu Ibrahim ya tabbatar da kakkabe barazanar mutanen da kuma wannan mazaunin nasu a Sokoto.

Mawallafi: Aminu Abdullahi Abubakar
Edita: Pinaɗo Abdu Waba