Mutane sun mutu a rikicin zaben Indonesiya | Labarai | DW | 23.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane sun mutu a rikicin zaben Indonesiya

'Yan sanda sun ce kura ta lafa a birnin Jakarta bayan kame daruruwan mutane da ake zargi da haddasa rikicin, amma akwai sauran kallo kan matakin dan takara Prabowo Subianto na kalubalantar sakamakon zaben.

'Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutane bakwai a Jakarta babban birnin kasar Indonesiya bayan barkewar rikici sakamakon zanga-zangar lumana kan ayyana Shugaba Joko Widodo a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar.

Wannan dai shi ne karo na biyu da Shugaba Widodo ke kada abokin takararsa Prabowo a takarar shugabancin Indonesiya, amma 'yan adawa na zargin gwamnati ta amfani da ikonta wajen yin magudin zabe.