Mutane sun halaka a rikicin ′yan Shi′a da jami′an tsaro a Najeriya | Labarai | DW | 13.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane sun halaka a rikicin 'yan Shi'a da jami'an tsaro a Najeriya

An dai rika jin kararraki na bindiga da ababan fashewa cikin daren Asabar a garin na Zariya a jihar Kaduna da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

Nigeria Soldaten

Dakarun sojan Najeriya

A wutar rikici da ke ruruwa tsakanin ‘yan Shi'a a duk fadin Nijeriya da jami'an tsaro musamman ma dai sojoji. Shugabanninsu, sun umurci mabiyansu, su bazama kan tituna don nuna rashin amincewa da harbin da sojoji suka yi wa mabiyan na su a Zaria cikin daren Asabar.

Malam Yakubu Yahaya da ke zama mabiyin wannan tafarki da suma suka gudanar da tasu muzaharar a jihar Katsina Arewa maso Yammacin na Najeriya ya ce tun cikin daren ranar ta Asabar ne lamarin ya munana abin da ya sanya ba za su iya bada kiyasin mutanen da suka rasu ba.

An dai rika jin kararraki na bindiga da ababan fashewa cikin daren na Asabar a garin na Zariya da ke zama babbar cibiya ga mabiya wannan tafarki a Najeriya.

A ranar ta Asabar dai mai magana da yawun jami'an sojan na Najeriya ya bayyana cewa mabiyan na tafarkin na Shi'a sun bude wuta ga jerin gwanon shugaban rundunar sojin Janar Tukur Burutai.