1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane nawa ne suka mutu sakamakon yaƙin Iraƙi

November 19, 2007

Ƙididdiga akan yawan Mutanen da suka mutu sakamakon yaƙin Iraƙi

https://p.dw.com/p/CJCs
Bush da Sojojin ƙawance a IraƙiHoto: AP

Masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkanmu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na Amsoshin takardunku, shirin da a kowane mako yake amsa wasu daga cikin tambayoyin da kuka aiko mana.

Abdullahi: Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun Malam Habibu Lawan daga birnin Abuja a tarayyar Najeriya; Malamin cewa ya yi; Don Allah ina so ku sanar da ni yawan Mutanen da suka mutu sakamakon yaƙin Iraƙi, tun daga ranar da aka ƙaddamar da shi ya zuwa yanzu.

Abba: To Abdullahi idan ana batun mace-mace a Iraƙi to fa ana batu ne akan ɓangarori guda biyu, wato ɓangaren sojojin mamaya na Amurka da ƙawayenta da kuma ɓangaren al’ummar Iraƙi da ‘yan-gwagwarmaya

To a ɓangaren sojojin Amurka da ƙawayenta ƙididdiga ta nuna cewa tun daga ranar da aka fara yaƙin Iraƙi zuwa ranar juma’ar nan, an kashe sojojin ƙawance kimanin 4,200. Kai a dangane da wannan batu ma na mutuwar sojojin ƙawance, kamfanin yada labarai na CNN ya samar da wani shafi a Duniyar Gizo wato (INTERNET) wanda a kullum yake sabunta cikakkiyar ƙididdigar sojojin kowace ƙasa da suka mutu, kuma bayanan sun haɗa har da sunan sojan da ya mutu da hotonsa da shekarunsa da yankin da ya ke a Iraƙin da ma sunan garinsa da ƙasarsa.

Abdullahi: To abin mamakin shine a ɓangaren al’ummar Iraƙi babu wata sahihiyar ƙididdiga da take nuna gaskiyar yawan al’ummar da suka mutu a Iraƙi tun daga su kansu ‘yan gwagwarmayar har zuwa kan jama’ar gari waɗanda ake kashewa kulli yaumin. Kai karshen magana dai an ruwaito jagoran sojojin mamayen na Iraƙi wato General Tommy Franks yana cewa “Ba ma ɗaukar wata ƙididdiga na al’ummar Iraƙi da suka mutu’’.

Abba: Ko da yake a wajen kafafen yaɗa labarai al’ummar Iraƙi da suka rasa rayukansu basu wuce dubu 50-60 ba, a ƙididdigar da aka bayar ta watan octoban shekara ta 2006. To amma wani bincike da wata mujalla ta likitoci mai suna (lancet medical journal) ta bayar, ya nunar da cewa waccan ƙididdiga ta kafafen yaɗa labarai ba gaskiya ba ce. Domin kuwa a tata ƙididdigar an samu ƙarin mutane 650,000 akan na kafafen yaɗa labarai. Wato a gurin wannan mujalla mutane 700,000.suka mutu.

Abdullahi: Kuma fa Abba wannan ƙiyasi wata ƙungiyar masana ce a nan turai waɗanda suka sadaukar da kansu wajen yin bincike da kuma bayar da cikakken bayani akan mace-mace da wahalhalun da al’ummar Iraƙi ke ciki.

Abba: To ai idan aka yi filla-filla da bayan da wannan mujalla ta ƙunsa a ƙarkashin wannan ƙiyasi, ya tabbatarwa da Duniya waɗansu abubuwa guda biyar. Kaga na farko dai; A taƙaice ana yi wa dubun-dubatar al’ummar Iraƙi kisan gilla a kowace ranar Allah tun daga farkon shekara ta 2006 da ta gabata, kuma kashi 90 bisa 100 daga cikin waɗanda aka kashe ɗin, a hukumance ba a ma san da su ba.

Na biyu kuma kusan mutane 800,000 ko fiye da haka ne suka samu munanan raunuka ta hanyar tashin bama-bamai ko kuma tsananin azaba da suka sha sakamakon ɗauki ba dadi tsakanin sojojin mamaye da ‘yan gwagwarmaya, amma sama da kashi 90 bisa 100 a waɗannan mutane ba sa samun kulawa kuma ko da waɗanda aka kai Asibiti ma ba sa samun magani

Abdullahi: To Ina ganin na ukun shine yadda wannan ƙididdiga ta nuna cewar fiye da kashi 7 bisa 100 na ɗaukacin maza a Iraƙi an kashe su a tashin hankali, amma idan ana batun wuraren da abin ya fi muni irin su Falluja da Bagadaza ai abin ma ya zarce haka nesa ba kusa ba.

Sannan kuma wani batun shine kusan fiye da rabin miliyan na takardar shaidar rasuwa da aka rarrabawa iyalan waɗanda suka mutu , ba a shigar da su cikin lissafi ba a hukumance. Saboda haka basa cikin kididdiga.

Abba: To na biyar ɗin shine yadda bayanai suka nuna cewar; mutanen Iraƙin da sojojin ƙawance suka kashe daga farkon shekara ta 2006 zuwa tsakiyarta sun fi mutanen da aka kashe a shekarun baya yawa. To kaga kuwa wannan ta’annati ba ƙarami ba ne.

Abdullahi: In dai waɗannan bayanai suka tabbata gaskiya ne, hakan yana nuna kenan akwai sakaci ko rashin cancanta ko kuma yin shakulatin ɓangaro da jami’an hukumar Iraƙi suka yi na ƙin ɗaukar lissafin ƙididdigar mutanen da suke mutuwa da waɗanda suke samun raunuka tun daga lokacin da aka fara kai hari wannan ƙasa.

Abba: Sannan kuma abin duk ya taru ya ƙare akan mutane waɗanda basu ji ba ba su gani ba, musammman ma tsofaffi da mata da kananan yara, tun da ga shi bayanai sun nuna cewar mafi ƙanƙantar mutane da suka samu munanan raunuka yawansu ya haura 800,000.

Abdullahi: Har ila yau kuma zamu iya cewa sakamakon wannan bincike ya nuna gazawar ƙungiyoyin tallafi da na kare haƙƙin bil’adama waɗanda suka kasa samar da sahihan bayanai na haƙiƙanin gaskiyar halin da mutanen Iraƙi ke ciki musamman ma a ƙauyuka, in da ake zuwa ake samamen Samari da magidanta ba tare da sanin inda ake kai su ba.

Abba: To ai kafafen yaɗa labarai ma ba zasu tsira daga wannan zargi na ƙin sanar da ainihin gaskiyar halin da al’ummar Iraƙi suke ciki ba, musamman ma kafafen yaɗa labaran ƙasar Iraƙin da kuma na ƙasashen Duniya, wato ma’ana yadda kafafen yaɗa labarai suka ringa faɗin abin a watan farko na mamayar da aka yi wa iraki a 2003 bai kamata su sassauta ba kasancewar abin kullum gaba-gaba yake yi ba baya ba, fiye ma da yadda aka fara mamayar tun da farko.

Abdullahi: Kuma baya ga masu mutuwa kulli yaumin da masu samun raunuka, ɗaya batun da yake ciwa mutane tuwo a ƙwarya shine irin yadda ake kama mutane ake tsaresu a kurkukun Abu Ghraib da sauran gidajen kurkuku na ciki da wajen Iraƙi, da kuma uwa-uba irin azabar da ake gallaza musu wadda sakamakon haka ma wasu suke rasa rayukansu. Abin dai ba daɗin ji ba kyan gani.

Abba: Kuma fa zancen nan da muke da kai a yanzu haka, fiye da mutane 60,000 ne suke tsare a gidajen yari daban-daban a Iraƙi. Kamar dai yadda ƙungiyar agaji ta Red Cross ta sanar.

Abdullahi; Shi ya sa ni kullum nake ƙalubalantar Majalisar Dinkin Duniya, duk da cewa majalisar da farko ba ta amincewa Amurka da ƙawayenta su kai wannan hari ba, amma daga baya suka tilasta wa kwamitin sulhu na majalisar sai da ya fitar musu da ƙudurin da ya halatta musu wannan mamaya da goyon bayansa. Duk da cewa babban aikin wannan kwamiti anan shine hana yaɗuwar faɗace-faɗace da tabbatar da dakatar da wuta a yayin yaƙi, a taƙaice dai tabbatar da sulhu da zaman lafiya a duk fadin Duniya.

Abba: To kaga babban abin tambaya anan shine, al’ummar Iraƙi da aka mamaye su, ina za su kai ƙarar waɗanda suka mamaye musu ƙasa? Shin a irin halin da kwamitin sulhu na majalisar dinkin Duniya yake ciki yanzu, kai shin yana ma da ƙarfin ya saurari kukan ƙasashen da ake zalunta kuwa? Wato matuƙar dai ba’a yi kwaskwarima ga tsarin Majalisar Dinkin Duniya ba, matuƙar dai ba’a soke haƙƙin hawa kujerar naƙi da wasu ƙasashe suke da shi ba, to babu yadda za a yi zukatan al’ummomin Duniya su kwanta da wannan majalisa.

Abdullahi: Yanzu Abba, abin ace zaka yi gaba da gaba da shugaba Bush, wace irin shawara zaka ba shi?

Abba: Shawarar da zan ba shi ita ce, Ya mai da hankali akan matsalolin da suka shafi jama’ar Amurka ba wai ya riƙa yin katsalandan a harkokin wasu ƙasashe ba. Sannan kuma ya kula da shugabancin kasarsa, ya sani cewa ƙasarsa ta Amurka ita ce kasar da tafi kowacce ƙasa cin bashi a Duniya, saboda haka miliyoyin dalolin da yake kashewa a waje domin su yi yaƙi ya juya akalasu ya biya basussukan da ake bin ƙasarsa, domin kuwa yaƙin da yake yi bashi da wani alfanu ga al’ummar Amurka. Sannan kuma su kansu al’ummar Iraƙin da ya ce dansu ya ke yi, sun tabbatar da cewa wannan yaƙi ba shi da wani alfanu a garesu, sai ma jefa su da yayi cikin bala’i.