Mutane kusan 30 sun hallaka a kasar Masar | Labarai | DW | 26.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane kusan 30 sun hallaka a kasar Masar

Rikicin da ya barke a kasar Masar tsakanin jami'an tsaro da masu zanga-zanga ya yi sanadiyar mutuwar mutane masu yawa

Dubban masu zanga-zanga a wannan Asabar (25. 01. 2014) sun yi macin tunawa da shekaru uku da yin juyin-juya halin da ya kawo karshen gwamnatin Hosni Mubarak ta shekaru 30.

Masu goyon bayan sojojin da suka kifar da gwamnati, sun nemi Janar Abdel-Fattah el-Sissi ya yi takaran neman shugabancin kasar. Amma a daya hannun an kai ruwa rana a tsakanin jami'an tsaro da 'Yan Kungiyar 'Yan Uwa Musulmai, wadanda aka yi amfani da karfi domin tarwatsa zanga-zangar. Akwai rahotannin da ke cewa kusan mutane 30 ne suka mutu sakamakon rikicin.

Tun bayan kifar da gwamnatin Mohamed Mursi cikin shekarar da ta gabata, rikicin siyasa na kasar ta Masar ya kara fadada.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Saleh Umar Saleh