Mutane kusan 30 ne suka mutu a Somalia | Labarai | DW | 09.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane kusan 30 ne suka mutu a Somalia

Jami´an gwamnatin Somalia sun sanar da rasuwar da yawa daga cikin yan kasar. Hakan a cewar su, ya biyo bayan wani hari ne da dakarun Amurka suka kai da jiragen yaki a kudancin kasar.

Tuni dai dakarun na Amurka suka ce sun kai harin ne da nufin halaka tsagerun kungiyyar Alqeda, da suke tunanin na da mafaka a kudancin kasar .

Daga cikin yan alqaedan da aka kai wannan hari domin su, a cewar rahotanni akwai madugun kungiyyar dake a gabashin nahiyar Afrika da kuma wanda ake zargi da dana bom din nan na ofishin jakadancin Amurka dake Kenya da Tanzania a shekara ta 1988.

Ya zuwa yanzu dai kafafen yada labarai sun rawaito ministan harkokin wajen kasar, Mr Ali Jama na nuna mihimmancin kai wannan hari da dakarun sojin na Amurka suka yi.

Ya zuwa yanzu dai rahotanni sun nunar da cewa mutane kusan talatin ne fararen hula suka rasa rayukan nasu, a sakamakon kai wannan hari.