Tattalin arziki
Mutuwa a wajen hakar ma'adanai na Afirka ta Kudu
December 8, 2019Talla
A Afrika ta Kudu mutane hudu sun mutu yayin da wani mutum guda ya jikkata bayan da dutse ya fada ya ruife su a a wajen da suke hakar ma'adinai, kamfanin da ma kungiyar masu hakar ma'adainai.
Kungiyar masu hakar ma'adainai ta kasar Afirka ta Kudu ba ta ji dadin yadda kamfanin da ke aikin a wajen ya gaza ba wajen samar da wata hanyar fita ba a lokacin aukuwar hadari irin wannan. Mai magana da yawun kungiyar ta masu hakar ma'adainai ya ce dutsen ya rufta ne biyo bayan wata girgizar kasa da aka samu a yankin.
Kamfanin na Village Main Reef da ya rasa ma'aikatansa ya ce ba zai ce komai ba har sai an gama fito da mutane da suka mutu an kammala bincike kafin su yi bayani.