Mutane goma sun halaka a wani rikici a Indiya | Labarai | DW | 27.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane goma sun halaka a wani rikici a Indiya

A cewar ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta Indiya cikin wadanda suka rasu akwai 'yan sanda uku da fararen hula uku.

Indien Angriff Polizeistation Punjab Dinanagar in Gurdaspur

'Yan sanda a jihar Punjab

Jami'an 'yan sanda a kasar Indiya sun sami damar shawo kan wani kazamin rikici a ofishin 'yan sanda a ranar Litinin din nan bayan da aka dauki tsawon sa'oi goma sha biyu ana musayar wuta da wasu mutane sanye da kayan sarki da bindigogi, rikicin da ya sanya mutane goma suka rasu a jihar Punjab kusa da iyakar kasar da Pakistan.

Firaministan kasar Indiya Narendra Modi da manyan ministocinsa sun ki bada cikakken bayani kan wannan hari wanda ake ganin idan ya shafi tsallaka iyakokin kasashen biyu ne zai iya tada tsohon rikici da ke a kwance tsakanin kasashen biyu.

A cewar ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta Indiya cikin wadanda suka rasu akwai 'yan sanda uku da fararen hula uku.

'Yan sandan sun ce an dauki lokaci ne ana musayar wuta da maharan saboda kokarin ganin an kama koda daya daga cikinsu a raye . Har ila yau 'yan sandan sun ce maharan sun tsallako ne daga kasar ta Pakistan kwanaki biyu da suka gabata.Tuni mahukuntan kasar ta Pakistan suka fito da yin Allah wadai da harin.