Mutane fiye da 60 sun mutu a harin bam a Kano | Labarai | DW | 28.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane fiye da 60 sun mutu a harin bam a Kano

Akalla mutane 64 ne suka rasu, wasu kuma 126 suka samu raunuka a harin bama-baman da aka kai a Masallacin Sarki da ke birnin Kano na Tarayyar Najeriya.

Daya daga cikin manyan asibitocin birnin na Kano ne ya karbi gawawwakin mutanen 64, yayin da wasu manyan asibitocin uku na birnin, suka karbi mutanen 126 da suka jikkata a cewar wani jami'in agajin gaggawa da bai so a bayyana sunan shi ba. Amma kuma ya ce adadin na iya karuwa nan gaba ganin yadda da dama daga cikin wadanda suka jikkata ke cikin mawuyacin hali.

Masallacin dai da ke tsakiyar birnin na Kano shi ne Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu ya ke yin limancin a cikinsa a duk ranakun Jumma'a. Wannan dai na zaman hari mafi muni da aka kai a kan wani masallaci a birnin na Kano. Rahotanni dai sun ce Sarkin na Kano yana wata kasar waje lokacin kai harin na wannan Jumma'a..

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita: Mohammad Nasiru Awal