Mutane fiye da 20 sun mutu a Potiskum | Labarai | DW | 03.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane fiye da 20 sun mutu a Potiskum

Rahotanni daga jihar Yobe a Najeriya na cewa, akalla mutane 23 ne aka tabbatar da cewa sun rigamu gidan gaskiya a harin kunar bakin waken da aka kai a Potiskum.

Harin dai an kaishi ne kan Musulmi mabiya mazhabar Shi'a da ke yin zanga-zangar lumana ta muzahara ranar Ashura da suka saba yi duk shekara domin tunawa da kisan gillar da aka yiwa Imam Hussaini jikan Annabi a lokacin yakin Karbala a kasar Iraki. Dan kunar bakin waken dai ya shiga cikin masu muzaharar kafin daga bisani ya tashi bam din da ke jikinsa a tsakiyar su dai-dai wata kasuwa a garin na Potiskum da ke jihar Yobe wadda ke fama da tashe-tashen hankulla na Boko Haram.

A wani labarin kuma a daren wannan Lahadin ne wasu mutane dauke da makamai suka kai hari a wani gidan kaso na birnin Lokoja dake jihar Kogi, inda suka kashe mutum guda tare da fitar da firsinoni a kalla 144. Adams Omale shine jagoran masu tsaron wannan gidan kaso kuma ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce a halin ynzu an yi nasarar kamo 26 daga cikin firsinonin da suka tsere din.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu