Mutane da yawa sun mutu a guguwar Vanuatu
March 15, 2015Talla
Mutane da dama dai sun rasa rayukansu a wannan guguwa mafi tsanani da ke tafiyar km 250 a kowace sa'a guda.
Wannan bala'i daga indallahi dai ya lalata sama da kashi 90 cikin 100 na gidajen wannan tsibiri. A yanzu haka kungiyoyin agaji na nazarin irin asara ad aka yi, tare da kokarin kai kayayyakin agaji zuwa yankun da ke da wahalar isa.
Shugaban tsibirin Baldwin Losdale da ke halartar taron MDD kan rage hadari a Japan , ya yi kira da a kai wa jama'arsa dauki, sakamakon hali mawuyaci da suka tsinci kansu a ciki bayan mummunar guguwar da aka yi wa lakabi da suna Pam.