Mutane da dama sun rasu a wani mummunan faɗa a lardin Waziristan | Labarai | DW | 07.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane da dama sun rasu a wani mummunan faɗa a lardin Waziristan

Rundunar sojin Pakistan ta ce an kashe wasu ´yan takife kimanin 50 da kuma sojoji 20 a wani kazamin fada da aka gwabza a yankin arewa maso yammacin kasar. Rundunar ta ce an gwabza fadan ne a lardin arewacin Waziristan mai kwarya-kwaryar ´yancin cin gashin kai bayan da ´yan tawaye suka kai harin kan wani ayarin motocin soji. Wannan yanki dai dake kan iyaka da Afghanistan na zama wani sansani na magoya bayan kungiyar Taliban da ´yan ta´addan kungiyar al-Qaida.