1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Girgizar kasa ta hallaka mutane 142 a Indonisiya

Abdullahi Tanko Bala
August 6, 2018

Yawan mutane da suka rasu a girgizar kasa a Indonisiya na karuwa yayin da ma'aikatan ceto ke ci gaba da kokarin zakulo mutanen da lamarin ya ritsa da su.

https://p.dw.com/p/32fDy
Vulkan Lombok Evakuierung Bergsteiger
Aikin ceto bayan girgizar kasa a IndonisiyaHoto: picture-alliance/dpa/V. Sanovri

Akalla mutane 142 suka mutu a girgizar kasa mai karfi a Indonisiya.

Hukumomi sun ce girgizar kasar ta jijjiga tsibirin Bali kuma har yanzu masu aikin ceto basu sami kaiwa wasu yankuna da ke kan tsaunuka ba.

Wannan dai shine karo na biyu da aka sami girgizar kasa mai muni a cikin mako guda a yankin Lombok.

Jami'in hukumar agajin gaggawa na kasar yace girgizar kasar ta yi mummunar barna ta kuma ragargaza daruruwan gidaje.

Ana dai yawan samun girgizar kasa a Indonisiya inda ko da a shekarar 2004 girgizar kasa mai karfin maki 9.1 a ma'aunin Richter da ta auku a gabar tsibirin Sumatra ta haddasa igiyar ruwa da ta hallaka mutane dubu 230.