Mutane biyu sun mutu a zanga-zangar kenya | Labarai | DW | 06.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane biyu sun mutu a zanga-zangar kenya

'Yan adawa na nema a rusa hukumar zaben kasar Kenya. Wannan ya haddasa zanga-zangar da ta halaka rayukan mutane biyu a yammancin kasar.

Mutane biyu sun mutu yayin da wasu shida suka jikata a wata zanga-zanga da ya gudana a birnin Kismu da ke yammacin kasar kenya. 'Yan adawa ne suka shirya wannan sabuwar zanga-zanga don neman gwamnati ta rusa hukumar zaben kasar.

Shaidun gani da ido sun ce jami'an 'yan sanda sun yi harbe-harben kan mai uwa da wabi. Sai dai Sufeto Janar na 'yan sandan kenya Joseph Boinet ya ce sun tarwatsa zanga-zangar saboda haramtacciya ce.

Ya ce "Kotu ta gargadi duk kungiyoyin da ke da niyar shirya-shirya zanga-zanga da su fara neman izini daga hukumomi kasar tukuna. "