Mutane bakwai sun mutu a wani hari a Biu | NRS-Import | DW | 12.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

NRS-Import

Mutane bakwai sun mutu a wani hari a Biu

A Najeriya wasu mata biyu sun tayar da bam da ke jikinsu a garin Biu, lamarin da ya haddasa mace-mace da kuma samun rauni. Wannan shi ne karon farko da aka kai hari a garin.

Mutane kimanin bakwai sun mutu yayin da wasu karin 16 kuma sun jikata sanadiyyar tashin wani bam a kasuwar garin Biu na jihar Borno. Wannan dai shi ne karon farko da garin da ke kudancin jihar ya fuskanci harin kunar bakin wake tun bayan barkewar matsalar tsaro a Najeriya.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa da misalin karfe uku da mitin 20 na yammacin wannan Alhamis ne wannan bam ya tashi a kusa da wata mota. A cewar su wasu mata ne guda biyu suka tayar da bam din kuma suna cikin wadanda suka mutu.

Ya zuwa yanzu dai hukumomi ko jami'an tsaro ba su ce komai kan tashin bam din ba yayin da ake kulawa da wada da suka jikata a asibiti.