Mutane aƙalla 26 ne suka rasu a hare-hare a Iraƙi | Labarai | DW | 16.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane aƙalla 26 ne suka rasu a hare-hare a Iraƙi

Hare-haren 'yan Ƙungiyar IS a IraƘi sun yi sanadiyyar rasuwar mutane 26 a wannan Alhamis ɗin, yayin da wasu da dama suka jikkata, a birnin Bagadaza da kuma Mahmoudiyah.

Da farko dai wasu motoci ne biyu shake da bama-bamai suka tarwatse a Kazimiya da ke arewa maso yammacin birnin Bagadaza inda mutane 10 suka rasu tare da jikkata wasu 29, sannan wani ɗan ƙunar bakin wake ya tarwatsa motar sa a unguwar Talibiya cikin birnin na Bagadaza inda nan ma mutane tara suka rasu wasu kuma 26 suka jikkata, sai kuma a Mahmoudiyah da ke a nisan km 30 a kudancin binin na Bagadaza inda mutane aƙalla bakoye suka rasu.

A cewar Majalisar Ɗinkin Duniya aƙalla mutane 1100 ne suka mutu sakamakon hare-haren ta'addanci a ƙasar ta Iraƙi a watan Satumba da ya gabata, inda daga farkon watan nan na Oktoba kawo yanzu aƙalla wasu mutane 400 sun rasu sakamakon hare-haren.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Abdourahmane Hassane