Mutane 93 sun kamu da zazzabin Lassa a Najeriya | Zamantakewa | DW | 12.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Mutane 93 sun kamu da zazzabin Lassa a Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta bayyana daukar sabbin matakai na shawo kan zazzabin Lassa wanda aka samu karuwar mutanen da suka kamu da cutar da ma wadanda ta yi dalilin mutuwarsu.

Saurari sauti 03:12

Rahoto kan matakan yakar zazzabin Lassa a Najeriya

Sake bullar zazzabin wanda tun 1969 ya fara bulla a garin Lassa da ke jihar Borno ya sanya fuskantar barazana a fannin kula da lafiya, domin daga jihohi biyu a yanzu zazzabi ya kai ga bulla a yanki Kudu maso Yammacin kasar. Sannan kuma ya sanya gwamnatin kara mikewa tsaye domin yi ma zazzabin na Lasa tarba-tarba ta hanyar kafa kwamitin kwararru don ya kai ziyara a jihohin da cutar tafi kamari na jihohin Niger, Kano da kuma Bauchi.

Ministan kula da lafiya na Najeriyar Farfesa Isaac Adewale da ya jagorancci taron musamman don bayyana zahirin halin da ake ciki, ya bayyana cewa matakan da ake dauka sun taimaka shawo kan matsalar. To amma me ya sanya a bana matsalar tafi ta kowace shekara ta'azarra?

Lassavirus

Kwayar cutar zazzabin Lassa

Ya ce " ba’a sanar da ma’aikatar lafiya barkewar cutar da sauri ba: Alal misali a jihar Niger tun a watan Agusta aka samu bullar zazzabin na Lassa, amma sai a watan Nuwamba aka sanar da mu: Wannan abin takaici ne amma dai a yanzu muna da mutane 93 da muke zargin sun kamu da cutar, mutane 25 kuma mun tabbatar da kamuwarsu yayin da 41 sun mutu. Amma abin da ya bamu kwarin gwiwa a sa'o’I 72. Mun kama hanyar shawo kan cutar’’

Tun daga shekara ta 2002 ne zazzabin na Lassa ya ci gaba da karuwa daga mutane 55 da a yanzu ya kai fiye da mutane 1700 abin da ke zama babban kalubale ga mahukuntan Najeriyar, sanin cewa daukan mataki na kariya shi ne mafi alkhairi don kare lafiyar al’umma.

Sauti da bidiyo akan labarin