Mutane 60 sun halaka a harin ta′addanci a Yemen | Labarai | DW | 29.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 60 sun halaka a harin ta'addanci a Yemen

A kasar Yemen mutane 60 sun halaka a cikin wani kazamin harin kunar bakin wake da Kungiyar IS ta kai tun da sanhin safiyar wannan Litinin a birnin Aden.

Hukumomin tsaron kasar ta Yemen sun bayyana cewa an kai harin ne da wata mota da aka dana wa bam a wata cibiyar sojoji sabbin dauka da ke a bakin garin birnin Aden.Wasu shaidun gani da ido sun ce a lokacin da wata babbar motar dokar kaya ta shigo a cikin makarantar ne dan kunar bakin waken ya yi amfani da wannan dama inda ya kutsa da motar tasa a guje a cikin sajojin sabbin dauka a daidai lokacin da suka tattaru suna cika takardun shirin kama aiki bayan an dauke su.

Karfin tashin bam din ya haddasa rugujewar ginin wani baban aji da ke kunshe da tarin sojojin sabbin dauka. Wannan dai shi ne hari mafi muni da Kungiyar ta Is ta kaddamar a birnin na Aden tun bayan da sojin gwamnatin ta Yemen suka yi nasara kwato shi daga hannun 'yan tawayen kasar a wata Yulin shekara ta 2015.