Mutane 6 sun rasa rayukansu a Afghanistan. | Labarai | DW | 07.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 6 sun rasa rayukansu a Afghanistan.

Tashin wasu bamabamai guda 3 a Afghanistan, ya janyo asarar rayukan mutane 6, a cikinsu har da sojojin Amirka guda biyu. Tuni dai ’yan ƙungiyar Taliban, sun yi ikirarin dasa bamabamai a gefen titi a gabashin ƙasar, waɗanda tashinsu ne ya janyo mutuwar sojoji biyun na Amirka, da jin raunin wasu dakaru biyu kuma na ƙasar. A Kudu maso gabashin ƙasar, wani ɗan harin ƙunan baƙin wake, ya ta da bamabamai cikin motarsa, yayin da ya kutsa da ita cikin ayarin motocin sojin Amirka, inda a nan ma sojoji uku suka ji rauni.

Kazalika kuma, mutane 3 ne rahotanni suka ce sun sheƙa lahira a dai wannan yankin na kudu maso gabashin Afghanistan din, bayan da wasu bamabamai da ake shirin ɗaurawa kan babur a wata makaranta, suka yi bindiga.