Mutane 57 sun rasu a Pakistan | Labarai | DW | 11.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 57 sun rasu a Pakistan

Rahotanni daga kasar Pakistan na nuni da cewa wani hadarin mota da ya afku a kudancin kasar ya hallaka mutane 57 tare da jikkata wasu da dama.

Wata likita Dr. Seemi Jamali da ta tabbatar da faruwar lamarin ta ce a yanzu haka sun karbi gawarwaki 57 a bangaren bada agajin gaggawa na asibitin koyarwa na Karachi. Ministan sufuri na gundumar Sindh Mir Mumtaz Hussain Jakhrani ya ce hadarin da ya afku tsakanin wata mota kirar Bus da kuma tankar daukar mai ya faru ne yayin da motar kirar Bus kwace tare da yin taho mu gama da tankar daukar man da sanyin safiyar Lahadin nan a wani yanki da ke da nisan kilomita 50 da birnin Karachi na kasar ta Pakistan.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Usman Shehu Usman