Mutane 48 sun mutu a wani hari a Kenya | Siyasa | DW | 16.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Mutane 48 sun mutu a wani hari a Kenya

Wasu mutane da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Al-Shabab na Somaliya ne, sun kai hari a Mpeketoni na Kenya, inda suka kashe mutane da dama tare da lalata gine-gine.

A cewar ma'aikatan kungiyar agaji ta Red Cross da ke wannan yanki na Kenya, adadin mutanen da suka mutu sakamakon harin da ake kyautata zaton cewar 'yan kungiyar Al-Shabab ne suka kai shi, ya kai mutane 48. Yankin na Mpeketoni dai, na da nisan akalla km 100 da iyakar Somaliya. Sannan ya na da nisan km akalla 30 da da birnin nan mai tarihi na Lamu, wanda kungiyar mai kula da raya al'adu ta duniya, UNESCO ta ayyanashi a matsayin arzikin duniya.

Mutane 50 suka kai Hari.

Shaidun gani da ido dai sun tabbatar cewa, mutanen akalla 50, sun zo ne dauke da manyan makammai. Kuma suna dauke ne da tutar kungiyar Al-Shabab. Sannan suna maganar harshen Somali, tare da yin kabbara. Sai dai masu fashin baki na ganin cewa ba lallai ne a dora alhakin kai harin a kan kungiyar Al-Shabab ta Somaliya da ke gwagwarmaya da makamai ba kamar yadda wani lauya mai suna Ambrose Otieno da gidan talabijin din kasar ta Kenya yayi hira da shi ya bayyana.

Tuni dai kungiyar agaji ta Red Cross ta ce ta dukufa wajen lissafa adadin gidaje, ko hotel, da wuraren cin abinci, da ma motoci da maharan suka kokona. Kasar Kenya dai na fuskantar matsalolin hare-hare ne, tun bayan da dakarunta suka shiga kasar Somaliya a shekara ta 2011 domin yakar 'yan kungiyar ta Al-Shabab.

Mawallafi: Salisssou Boukari
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe