Mutane 44 sun rasu a tagwayen harin bam a Jos | Labarai | DW | 06.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 44 sun rasu a tagwayen harin bam a Jos

An kai hare-haren ne daya a wani masallaci lokacin tafsirin Al-Qurani dayan kuma wani gidan cin abinci.

Mutane fiye da 40 aka tabbatar sun rasa rayukansu sannan kuma wasu dama sun jikkata bayan tashin tagwayen bama-bamai a garin Jos, babban birnin jihar Filato da ke tsakiyar arewacin Najeriya, a daren Lahadi. Bam na farko ya tashi ne a wani wajen cin abinci da ke kusa da tashar Bauchi, da aka fi sani da Shagalinku, yayin da bam na biyu ya tashi a masallacin 'Yantaya lokacin da ake tafsiri, inda daruruwan al'ummar musulmi suka taru suna sauraron karatun Al'qurani. Hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa wato NEMA ta tabbatar da mutuwar akalla mutane 40 sannan wasu 67 sun jikkata a tagwayen hare-haren na ranar Lahadi da daddare. A kwanakin nan dai aiyukan 'yan tarzoma sun ta'azzara a arewacin Najeriya.