Mutane 42 sun mutu a hadarin mota a Faransa | Labarai | DW | 23.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 42 sun mutu a hadarin mota a Faransa

Hadarin ya wakana ne wami taho mu gama tsakanin wata motar da bus dauke da fasinja a cikin karamar hukumar Puisseguin da ke a Kudu maso Yammacin kasar

China Verkehrsunfall

A kasar Faransa mutane 42 sun halaka a cikin wani hadarin motocin da ya wakana a wannan Jumma'a a cikin karamar hukumar Puisseguin da ke a Kudu maso Yammacin kasar. Hadarin ya wakana ne bayan da aka yi taho mu gama tsakanin wata motar kudubale ta daukar itace da kuma wata motar bus dauke da fasinja wadanda akasarinsu tsaffin ne da ke kan hanyarsu ta zuwa shakatawa a wasu guraren dazukan kasar.

Motocin dai sun kama da wuta ne nan take a lokacin karon nasu. Mutane takwas sun tsira daga hadarin sai dai da dama daga cikinsu sun ji rauni wasunsu ma munana. Wannan dai shi ne hadarin mota mafi barna da ya wakana a kasar ta Faransa a cikin shekaru 33 na baya bayan nan.