SiyasaJamus
Mutane 40 sun mutu a wani hari a Nijar
March 22, 2021Talla
Jami'an tsaro a yankin Tahoua sun ce wasu a kan babura da ake zargin 'yan bindiga ne sun kai hari kauyuka uku da ke yankin a ranar Lahadi. Ko a ranar 15 ga watan Maris din shekarar 2021 ma mutane 66 sun rasa rayukansu a yankin da ke zama iyakar kasashen Nijar da Burkina Faso da Mali, yankin da ya yi kaurin suna wajen kai hare-haren ta'addaci.