Mutane 40 sun hallaka a hare-haren Iraki | Labarai | DW | 03.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 40 sun hallaka a hare-haren Iraki

Kimanin mutane 40 suka riga mu gidan gaskiya sakamakon hare-hare na kunar bakin wake da aka kai wasu yankunan 'yan Shi'a da ke birnin Bagadazan kasar Iraki.

Flames rise from a vehicle at the site of a car bomb in Talibiya in Baghdad on September 3, 2013. Car bombs ripped through mostly Shiite neighbourhoods of Baghdad, killing at least 40 people and wounding more than 100. AFP PHOTO/SABAH ARAR (Photo credit should read SABAH ARAR/AFP/Getty Images)

Irak Anschlagsserie September 2013

Jami'an tsaro dai sun ce motoci takwas ne makare da bama-bamai suka tashi a yankuna daban-daban na Bagadazan, kuma wannan ibtila'i ya faru ne kusan lokaci daya, daidai sanda jama'a ke zazzaune a wuraren shan shayi kamar da aka saba da yammaci a birnin.

Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai hare-haren da ma dai dalilin yin hakan sai dai mabiyya tafarkin Sunnah a birnin sun ce suna zargin wadanda ke da alaka da kungiyar nan ta Al-Qaida da kai harin.

A dan tsakannin dai Iraki na shan fama da hare-hare makamantan wannan, inda mahukuntan kasar suka ce suna aiki ba dare ba rana wajen kawo karshensa.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu