1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane 30 sun rasu a wani hari a Libya

Yusuf BalaFebruary 20, 2015

A cewar wani dan majalisa alamu na nuna cewar harin wani ramuwar gayya ne kan hare-hare da dakarun sojan kasar Masar suka kai kan mayakan IS a yankin Derna na kasar ta Libya,

https://p.dw.com/p/1Ef9d
Explosion einer Autobombe nebst der ägyptischen Botschaft in Tripolis
Hoto: M. Turkia/AFP/Getty Images

Fiye da mutane talatin ne suka rasu bayan da wata mota dauke da ababan fashewa ta tashi bam a birnin Qubbah na kasar Libya a ranar Juma'an nan kamar yadda Aguila Saleh dan majalisa da ya fito daga yankin ya bayyana.

Saleh ya bayyana wa gidan talabijin na Al- Arabiya cewa motar makare da bama- bamai ta nufi wani gidan mai ne da ke da kusanci da ofishin jami'an tsaro .

A cewar dan majalisa Saleh, alamu na nuna cewar harin wani ramuwar gayya ne kan hare-hare da dakarun sojan kasar Masar suka kai kan mayakan IS yankin Derna na kasar ta Libya, wanda kuma ke da kusanci da garin na Qubbah.

Tuni dai mahukunta a yankin suka bayyana zaman makoki na kwanaki bakwai a yankin na Qubbah dan nuna alhaini ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu.