Mutane 29 sun rasu a wani harin kunar bakin wake a Pakistan | Labarai | DW | 08.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 29 sun rasu a wani harin kunar bakin wake a Pakistan

An kai harin ne lokacin jana'izar wani dan sanda a Quetta, hedkwatar lardin Baluchistan dake zama tungar sojojin sa kai da kungiyoyin mayakan 'yan tawaye irin su Taliban.

Wani dan harin kunar bakin wake ya hallaka akalla mutane 29 ciki har da 'yan sanda biyar a wurin jana'izar wani dan sanda a birnin Quetta, a wani lamari da aka gani kai tsaye ta gidajen telebijin kasancewa kyamarorin tashoshin telebijin din na watsa jana'izar, a wannan Alhamis. Wakilin kamfanin dillancin labarun Reuters ya ce an shiga rudani inda aka dauki jami'an 'yan sanda i jina-jina cikin motocin daukar marasa lafiya. An dai tabbatar da mutuwar mutane 29 sannan 62 sun jikata, inji Babar Yaqoob Fateh Mohammed babban sakataren lardin Baluchistan. Daga cikin wadanda wannan ta'asa ta rutsa da su har da yara dake halartar jana'izar da kuma mukaddashin sifeto-janar na 'yan sanda birnin Quetta, Fayyaz Sumbal. An ga 'yan sanda suna kuka lokacin da suke neman gawarwakin abokan aikinsu da suka tarwatse, wasunsu kuma shiru suka yi a zaune saboda kaduwa. Kawo yanzu ba a san wadanda ke da alhakin kai wannan hari ba, sai dai Quetta dake zama shelkwatar lardin Baluchistan, sansani ne na sojojin sa kai ciki har da 'yan kungiyar Taliban da mayakan kungiyoyin 'yan tawaye.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu