Mutane 28 sun rasu a zanga-zangar Masar | Labarai | DW | 06.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 28 sun rasu a zanga-zangar Masar

Kimanin mutane 28 ne hukumomin Masar suka ce sun rasu sanadiyyar wani rikici da ya biyo bayan zanga-zangar da magoya baya da masu adawa da shugaba Mursi suka yi.

Rahotanni daga kasar Masar na cewar kimanin mutane 28 ne suka rasu yayin da wasu 94 suka jikkata a wannan Lahadin a wata taho mu gamar da aka yi tsakanin magoya bayan hambararren shugaban kasar Muhammad Mursi da masu adawa da shi.

Gidan talabijin din kasar ya rawaito wani jami'in tsaro na cewar gawarwakin mutanen da suka rasun na da harbin bindiga a jikinsu.

Ya zuwa yanzu dai gwamnatin kasar ba ta ce uffan ba game da wannan balahira da ta auku.

A jiya ne dai gwamnatin ta gargadi al'ummar kasar da su guji yin zanga-zanga da suka dau aniyar yi yayin da a yau ake cika shekaru 40 da samun wata nasara da Masar ta yi a wani yaki da ta yi Izra'ila, gargadin da wasu jama'ar suka yi watsi da shi.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman