1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Arzikin masu kudi na karuwa a duniya

Gazali Abdou Tasawa
January 21, 2019

Wani rahoto da Kungiyar Oxfam ta fitar ya nunar da cewa a shekara ta 2018 da ta shude arzikin duniya ya ci gaba da kasancewa a hannun wasu mutane kalilan.

https://p.dw.com/p/3Bsp4
Uk Oxfam-Sex-Skandal | Logo
Hoto: picture alliance/AP Photo/N. Ansell

Rahoton kungiyar wacce ke yaki da talauci da kuma tabbatar da adalci a duniya ya ce, wasu manyan attajiran duniya su 26 ne ke mallakar kimanin kaso 50 daga cikin 100 na tattalin arzikin mutane miliyan 1,800 da suka fi talauci a duniya. Kungiyar ta Oxfam ta ce gibin da ke da akwai a yanzu tsakanin masu arziki da sauran al'umma da ke fama da talauci a duniya na tauye kokarin da ake na rage kaifin talaucin a duniya, kana yana yin illa ga tattalin arzikin duniyar tare da kara haddasa takaici a zukatan al'umma.

Kungiyar ta Oxfam dai ta yi kira ga kasashe da su kara haraji kan masu arziki da kuma yin amfani da wannan kudi na haraji a fannin kiwon lafiya da na ilimi da samar da sauran ababen more rayuwa ga kowa da kowa. A shekara ta 2017 mutane 43 ne ke matsayin attajirai a duniya, adadin da a shekara ta 2018 ya dawo zuwa mutun 26 kacal, wanda ke nuni da irin yadda sannu a hankali arzikin duniyar ke kara tarewa a hannun wasu mutane kalilan.